TASIRIN HARSHEN BAYARWAWAJEN FASSARA TATSUNIYA: NAZARI DAGA TASKARTATSUNIYOYI NA BUKAR USMAN

Authors

  • Muhammad Rabiu Tahir Ahmadu Bello University, Zaria Author

Keywords:

Fassara, Tatsuniya, Hausa, Bukar Usman

Abstract

Manufar wannan takarda ita ce nazari a kan ƙalubalen da mai fassara yake fuskanta yayin aikin fassara, musamman daga harshensa na uwa zuwa wani harshe na daban. Wannan takarda ta nazarci Taskar Tatsuniyoyi na Bukar Usman wanda ya fassara tatsuniyoyin harshensa na Babur zuwa Hausa da nufin taskace al’adu da harshen al’umarsa. Baya ga yin bita a kan ayyukan fassara masu alaƙa da wannan bincike, an kuma zaɓi wasu daga cikin tatsuniyoyi 315 da mawallafin ya fassara aka karanta su, sannan aka ƙalailaice su. An yi amfani da mahangar al’ada da kuma ta harshe da ke duba ga tasirin mai fassara da kuma al’adun harshen bayarwa a kan harshen karɓa. Binciken ya zaƙulo kalmomi da al’adun da suka yi kutse cikin harshen Hausa sakamakon yin fassarar.

Downloads

Published

2022-12-01

Issue

Section

Articles